Zukata sun cika da tsoro a APC kan zaben fidda gwani

Zukata sun cika da tsoro a APC kan zaben fidda gwani

Gabannin zaben fidda gwamnatinta da aka shirya, zukata na cigaba da kasancewa cikin tsoro a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki yayinda kawunan yan jam’iyyar ke cigaba da rabewa kan tsarin zabar dan takara a zaben shekara mai zuwa.

Hakan na zuwa ne duk da cewar ana sanya ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gurfana a gaban kwamitin tantancewa na APC a yau, Alhamis, 20 ga watan Satumba domin kare kudirinsa na sake takara a 2019.

APC ta rabu kan tsarin zaben fidda gwani da za’a gudanar tsakanin na kato bayan kato da kuma na amfani da wakilai wajen zabar dan takarar jam’iyyar.

Zukata sun cika da tsoro a APC kan zaben fidda gwani

Zukata sun cika da tsoro a APC kan zaben fidda gwani
Source: Facebook

Yayinda kwamitin masu ruwa da tsaki ta umurci jam’iyyar da tayi amfani da zaben fidda gwani na kato bayan kato wajen zabar yan takaranta na kujerun, shugaban kasa, gwamnati, majalissun dokoki da na jiha, gwamnoni sun fi son ayi amfani da wakilai wajen zabar yan takara.

KU KARANTA KUMA: Zainab Ahmed ministar kudi ce – Fadar shugaban kasa

A kokarinsu na kawo karshen wannan rikici, gwamnonin APC sun yi ganawa na tsawon wasu sa’o’i a Abuja a daren jiya, Laraba, 19 ga watan Satumba.

An tattaro cewa gwamnonin sun yanke shawarar amfani da tsarin zaben fidda gwanin guda biyu, ya danganta da wanda jihar mutum tayi na’am dashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel