Zaben fitar da gwani: Oshiomhole da gwamnonin APC sun saka labule

Zaben fitar da gwani: Oshiomhole da gwamnonin APC sun saka labule

- Gwamnonin jam'iyyar APC sun shiga wata muhimmiyar taro jiya a Imo

- Ciyaman din jam'iyya, Adams Oshiomhole shima ya hallarci taron

- An kyautata zaton za su tattauna kan tsarin da za ayi amfani dashi ne wajen zaben fitar da gwamni

Mun samu daga Punch cewa gwamnonin jam'iyyar APC sun gudanar da wata taron sirri a gidan gwamnatin jihar Imo a daren jiya, cikin wanda suka hallarci taron har da gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode.

An gano cewa Ciyaman din jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole shima ya hallarci taron da aka fara misalin karfe 7.45 na daren jiya.

Zaben fitar da gwani: Oshiomhole, Ambode da gwamnonin APC sun saka labule

Zaben fitar da gwani: Oshiomhole, Ambode da gwamnonin APC sun saka labule
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Har yanzu dan na da ya mutu na amfani da bandakinmu kowanne dare - Mahaifiya

Duk da cewa ba'a san takamamen dalilin taron ba, an gano cewa gwamnonin sun kira taron ne domin tattaunawa kan irin tsarin da za'ayi amfani dashi wajen zaben fitar da gwani a jihohinsu da zaben 'yan kwamiti.

A baya, kwamitin zartarwa na APC ta amince da zaben 'yar tinke wajen zaben fitar da gwani amma da bawa jihohin zabin 'yar tinke ko kuma amfani da wakilai wato delegate wajen yin zaben fitar da gwanin.

A cikin kwana-kwanan nan, Shugaban jam'iyya na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana rashin goyon bayansa kan tazarcen gwamna mai ci a Legas, Akinwumni Ambode duk da rokon da wasu jiga-jigan jam'iyyar su kayi.

Tinubu da magoya bayansa a jihar Legas suna goyon bayan Babajide Sanwo-Olu ne tuni wanda tuni ma ya saya fom din takararsa a ranar Talata da ta gabata. Ciyamomi 57 a jihar sun bayana goyon bayansu ga Sanwi-Olu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel