PDP tayi kira kan kawo karshen shugabancin APC a jihar Osun

PDP tayi kira kan kawo karshen shugabancin APC a jihar Osun

A yayin zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a karshen wannan mako, jam'iyyar adawa ta PDP ta yi raddi na kira kan kawo karshen shugabancin jam'iyyar APC da a cewa ba bu abinda ta tsinanawa al'ummar jihar face jefa su cikin hali na tagayyara.

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun yi kira ga al'ummar jihar Osun akan su tabbatar sun kawo karshen wahalhalu da cuzguni da jam'iyyar APC ta jefa su cikin sa.

Manema takarar shugaban kasar biyu a karkashin jam'iyyar PDP, sun fadakar da al'ummar jihar akan romon dimokuradiyya da zai kwarara cikin jihar muddin suka kada kuri'unsu ga dan takarar kujerar gwamnatin jihar na jam'iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke a yayin zaben da za a gudanar a ranar Asabar 22 ga watan Satumba.

PDP tayi kira kan kawo karshen shugabancin APC a jihar Osun
PDP tayi kira kan kawo karshen shugabancin APC a jihar Osun
Asali: Twitter

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Atiku da Saraki sun yi wannan kira tare da fadakarwa yayin wani gangami na jam'iyyar su ta PDP da aka gudanar a birnin Osogbo na jihar ta Osun.

Saraki wanda a kwana-kwanan nan ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa ta PDP ya bayyana cewa, jihar Osun na daya daga cikin jihohin da suka fuskanci na tsanani na shugabancin APC musamman ta bangaren rashin biyan ma'aikata albashinsu, inda ma'aikata ke zaman kiradado da jiran albashin su har na tsawon shekaru uku.

KARANTA KUMA: Bafarawa ya bayyana dalilin da ya sanya yake son kasancewa shugaban kasar Najeriya

Atiku da Saraki sun yi tarayya da juna wajen kira ga al'ummar jihar akan su kada kuri'un su ga dan takara na jam'iyyar PDP tare da tabbatar da an gudanar da zaben na adalci da ya tsarkaka daga dukkan wani nau'ina magudi ko rashin gaskiya.

Kazalika, Saraki ya bayyana takaicin sa kwarai da aniyya dangane da yadda gwamnatin APC ta rike makogoron albashin ma'aikata har na tsawon shekaru uku, inda ya buga misali da gwamnonin yankin Arewa maso gabashin kasar nan da ba su gaza ba wajen biyan albashin ma'aikatansu duk da irin tsanani na ta'addanci da suke fuskanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel