Gwamna Ganduje ya gargadi sabon mataimakinsa kan abinda dayake bukata daga wajensa

Gwamna Ganduje ya gargadi sabon mataimakinsa kan abinda dayake bukata daga wajensa

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana abin dayake bukata daga wajen sabon mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna bai wuce tsantsar biyayya ba tare da hada shi da wani ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba 19 ga watan Satumba a yayin bikin nadin Gawuna a matsayin sabon mataimakinsa, inda yace sai da ya tace ya rairaye kafin ya zabo Gawuna.

KU KARANTA: Dan bindiga ya halaka mutane 9 a yayin bikin murnar kammala karatun jami’a a jahar Edo

“Yau rana ce mai matukar muhimmanci a garemu, idan zaku tuna a kwanakin baya ne mataimakina ya yi murabus don kansa, don haka ya bar mana gibi, amma cike wannan gibi ba karamin lamari bane don yana bukatar zabo mutumin da yafi dacewa da mukamin.

Gwamna Ganduje ya gargadi sabon mataimakinsa kan abinda dayake bukata daga wajensa

Gwamna Ganduje da Gawuna
Source: Facebook

“Don haka muka dauki tsawon lokaci muna gudanar da binciken kwakwaf don tacewa daga karshe muka zabo wannan mutumin, yana da digiri na biyu a fannin kimiyya, ya taba zama zababben shugaban karamar hukuma sau biyu, ya taba zama kwamishinan a Kano sau biyu.

“Hanya daya muka bi, domin nima na taba zama sakataren karamar hukuma, na zama shugaban karamar hukuma, na zama kwamishina na tsawon shekaru shida, mataimakin gwamna na tsawon shekaru takwas, don haka kunga kenan akwai kamanceceniya a tsakaninmu.” Inji shi.

Bugu da kari Ganduje ya kara da cewa mukamin mataimakin gwamna na bukatar tsantsar biyayya da kuma kyakkyawar niyya, tana bukatar mutum ya kasance jajirtacce kuma ma’aikaci, tana bukatar mutum ya zamo ya san sauye sauyen da siyasar Kano take dauka sa’annan sai mutum ya iya kware wajen tafiyar da gwamnati.

Daga karshe Ganduje ya tabbatar da dukkanin matakan kwarewarnan akan Nasiru Yusuf Gawuna, don haka ya umarce shi daya cigaba da rike mukamin kwamishinan harkar noma da albarkatun kasa na jahar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel