Zaben 2019: Jerin yawan mutanen da ke neman tikitin takarar gwamna a PDP

Zaben 2019: Jerin yawan mutanen da ke neman tikitin takarar gwamna a PDP

Wani binciken da aka gudanar yana nuni ne da cewa akalla mutane 123 ne suka sayi fom din neman tikitin takarar gwamna a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya a zaben gama gari da za'a gudanar a shekarar 2019.

Mun samu wadannan alkaluman ne daga wata majiyar mu a babbar hedikwatar jam'iyyar ta PDP dake a garin Abuja bayan da aka sanar da rufe saida fom din a satin da ya gabata.

Zaben 2019: Jerin yawan mutanen da ke neman tikitin takarar gwamna a PDP

Zaben 2019: Jerin yawan mutanen da ke neman tikitin takarar gwamna a PDP
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An tsinci gawar Manjo Idris Alkali a Jos

Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa sudai wadannan mutanen suna son yin takarar gwamnan ne a jahohi talatin daga cikin talatin da hudun da ke garemu a Najeriya.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa sauran jahohin Najeriyar da ba za'ayi zaben gwamna ba a shekarar 2019 sun hada da Anambra, Bayelsa, Ondo, Kogi, Ekiti da Osun.

A wani labari kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun shigar da kara a wata kotun tarayyar Najeriya suna kalubalantar dan takarar zama gwamnan jihar Osun a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Sanata ademola Adeleke.

Laifukan da jami'an 'yan sandan ke tuhumar Sanatan dai sun hada ne da satar ansa a jarabawa, zamba cikin aminci, zama sojan gona da kuma tafka assha a lokacin yana makarantar Sakandare din sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel