Ko sama ko kasa an nemi kwantainoni cike da dala miliyan 60 an rasa

Ko sama ko kasa an nemi kwantainoni cike da dala miliyan 60 an rasa

Gwamnatin kasar Laberiya ta sanar da cewa tana gudanar da bincike akan abin da ya afku da manyan kwantainoni biyu cike da kudaden da aka buga a kasar waje kuma aka shigar da su kasar tsakanin watan Nuwamba da na Agustan bana, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

An tattaro cewa ko sam ko kasa an nemi kudaden, wadanda suka kasance takardar kudaden kasar da suka kai dala miliyan 60, an rasa.

Wani rahoto ya ce kwantainonin da suke makare da kudade sun bar tashar jirgin ruwan kasar a Monrovia, babban birnin kasar, a karkashin sa idon jami'an tsaro a watan Maris, kuma an zaci sun nufi babban bankin kasar ne, amma sun bace.

Ko sama ko kasa an nemi kwantainoni cike da dala miliyan 60 an rasa

Ko sama ko kasa an nemi kwantainoni cike da dala miliyan 60 an rasa
Source: Depositphotos

Har ila yau ba'a ga kudaden da aka kawo ta babban filin saukar jirage na kasa-da-kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kano ya rantsar da sabon mataimakin gwamna

Ma'aikatar shari'ar kasar ta nemi mutane da su kwantar da hankulansu yayin da wani kwamitin jami'an tsaro ke gudanar da bincike akan al’amarin.

Ministan watsa labarai, Eugene Nagbe, ya shaida wa gidan rediyon kasar cewar Shugaba George Weah, wanda aka rantsar a watan Janairu, ya nuna rashin jin dadi kan rashin sanar da shi matsalar a kan lokaci ba.

"Abin tashin hankali ne," in ji Mista Nagbe.

Kawo yanzu dai ba a kama kowa ba game da lamarin, amma ministan watsa labaran kasar ya ce yana da yakinin cewar za a gane hakikanin abin da ya faru a lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel