Dalilin gwamnatin tarayya ta dakatar da katafaren aikin farfado da 'Nigerian Air'

Dalilin gwamnatin tarayya ta dakatar da katafaren aikin farfado da 'Nigerian Air'

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da suka saka majalisar zartarwa ta kasa ta dakatar da aikin farfado da kamfanin jiragen sama na kasa (Nigerian Air) yayin zamanta na yau.

A cewar fadar shugaban kasa, kwamitin farfado da tattalin arziki na kasa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ke jagoranta ne bai amince da aikin ba.

Dalilin gwamnatin tarayya ta dakatar da katafaren aikin farfado da 'Nigerian Air'

Dalilin gwamnatin tarayya ta dakatar da katafaren aikin farfado da 'Nigerian Air'
Source: UGC

DUBA WANNAN: Za'a fara tilastawa 'yan Najeriya amfani da lambar dan kasa - FG

Rashin amincewar kwamitin ya samo tushe ne daga batun rashin ware kudi domin farfado da kamfanin na "Nigerian Air" da gwamnati ba ta yi ba cikin kasafin kudinta ba.

Shugaba Buhari ya shaidawa masu yunkurin ganin an dawo da Nigerian Air su nemi masu saka hannu jari da zasu saka kudi a bangaren domin ba zai amince da kashe kudin da gwamnati ba tayi kasafi da shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel