Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

- Saraki ya jagoranci gangamin goyon bayan dan takarar gwamna a Osun karkashin jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke

- Za’a gudanar da zabe ne a ranar Asabar 22 ga watan Satumba

- Daga cikin wadanda suka halarci gangamin harda Atiku, Gwamna Abdulfatai da kuma shugaban PDP na kasa, Uche Secondus

Gabannin zaben ranar Asabar, 22 ga watan Satumba da za’a gudanar a jihar Osun, shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba ya jagoranci gangamin goyon bayan dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) , Sanata Ademola Adeleke a Osogbo.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa tohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Shugaban PDP naa kasa, Uche Secondus, Gwamna Abdulfatai Ahmed na Kwara; mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Eddy Olafeso da sauransu sun bi sahun Saraki a gangamin wadda aka gudanar a Nelson Mandela Freedom Park dake Osogbo.

Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

Legit.ng ta tattaro cewa Saraki wanda ya kasance shugaban kamfen na jam’iyyar ya bukaci mazauna jihar da su zabi PDP a zaben da za’a gudanar.

Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

KU KARANTA KUMA: Kungiyar yan Najeriya dake zaune a kasar Amurka sun bukaci a bari su biya kudinfansar Leah Sharibu

Yace abun cin rai ne ganin gwamnatin APC mai mulki a jihar ta kasa biyan albashin ma’aikata na tsawon shekaru uku.

Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

Zaben Osun: Atiku, Saraki da Secondus sunyi gangamin goyon baya ga Adeleke

Saraki yace yana da tabbacin Adeleke zai lashe zabe sannan ya kawo karshen halin wahalar da mutanen Osun ke ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel