Rai daya ya salwanta yayin da 'Yan Baranda suka kai hari Birnin Gwari

Rai daya ya salwanta yayin da 'Yan Baranda suka kai hari Birnin Gwari

Dan sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, wani sabon harin 'yan baranda ya salwantar da rayuwar wani mutum guda, Abdulkarim Bagoma, da jikkatar wasu mutane uku a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Wannan hari ya auku ne bayan mako guda da aukuwar wani harin na 'yan baranda da suka yi garkuwa da wasu mutane bakwai da suka hadar da mata da kuma kananan yara a garin na Birnin Gwari.

Rahotanni sun bayyana cewa, daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da shi da kuma wani dan majalisar dokoki na jihar ta Kaduna, Salisu Haruna, sun samu sa'ar kubuta daga hannun 'yan ta'addan.

Sai dai kawowa yanzu shiru ake ji tamkar shuka ta ci shirwa dangane da rahoton wani ma'aikacin gidan talabijin na NTA, Isa Yahaya, wanda lamarin ya ritsa da shi da kuma iyalansa yayin safarar su.

Rai daya ya salwanta yayin da 'Yan Baranda suka kai hari Birnin Gwari

Rai daya ya salwanta yayin da 'Yan Baranda suka kai hari Birnin Gwari
Source: Depositphotos

A cewar wani shugaba na kungiyar tsaro da tabbatar da shugabanci na gari, Ibrahim Abubakar Nagwari, ya tabbatar da wannan lamari da ya auku a mahadar babbar hanyar Birnin Gwari ta jihar Kaduna da kuma hanyar garin Funtua ta jihar Katsina a ranar Talatar da ta gabata.

A jawaban Nagwari, ya bayyana cewa rayuwar wani Matashi, Abdulkarim Bagoma, ta salwanta yayin wannan hari inda kawowa yanzu ba wani amo ballantana labari dangane da inda wani matashi, Ibrahim Mai-Alignment ya shiga.

KARANTA KUMA: Fidda Gwani: Dalilin da ya sanya muka yi watsi da Zaben 'yar tinke - APC Adamawa

Ya ci gaba da cewa, mutane ukun da suka jikkata yayin wannan mummunan hari na ci gaba da samun kyakkyawar kulawa a wani asibitin kurkusa da aka garzaya da su cikin gaggawa.

Kazalika Nagwari ya bayyana takaicinsa dangane da yadda 'yan barandan da dakarun soji suka fatattako daga jihar Zamfara ke kustowa cikin jihar ta Kaduna, inda suke zartar da ta'ddanci kan al'umma ba tare da wani hakki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel