Dan bindiga ya halaka mutane 9 a yayin bikin murnar kammala karatun jami’a a jahar Edo

Dan bindiga ya halaka mutane 9 a yayin bikin murnar kammala karatun jami’a a jahar Edo

Akalla mutane tara ne suka gamu da ajalinsu a daidai lokacin da wasu daliban ajin karshe na jami’ar jahar Edo, Ambrose Ali University yayin da suke gudanar da bikin murnar kammala karatun jami’a.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin mutane tara da aka kashe akwai dalibai guda shidda da ake taya murnar kammala digirin nasu, ciki har da wani Chibudum Eistein wanda yake murnar kammala digiri a likitanci, yayin da sauran mutane uku tsofaffin daliban jami’ar ne.

KU KARANTA: Masu zanga zanga sun hana sabuwar ministar kudi shiga Ofis a Abuja

Shi dai wannan biki da aka fi sani da suna Party an shirya shi ne a wani gida dake titin Ihimudun a unguwar Ekpoma cikin karamar hukumar Esan ta kudu, kamar yadda wani jami’in karamar hukumar ya tabbatar, inda yace mamatan sun hada da maza da mata.

Wata majiya ta bayyana cewa wani dan bindiga ne daga cikin daliban makarantar ta bude ma daliban wuta yayin da suke tsaka da holewa sakamakon rigima da aka samu tsakaninsa da wani daga cikin daliban akan wata buduruwa.

Majiyar ta kara da cewa sakamakon rikicin da aka samu, sai dalibin ya fita daga wajen bikin cikin fushi, inda fitarsa keda wuya sai ya dawo da wasu gungun matasa dauke da bindiga, inda kafin a ankara sun bude musu wuta.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin jami’ar ya ci tura, haka nan shima kaakakin rundunar yansanda jahar yaki yace uffan game da lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel