Jirgin kasa ta tattake wani jami’in Dansanda a jahar Legas

Jirgin kasa ta tattake wani jami’in Dansanda a jahar Legas

Wani jami’in Dansanda mai mukamin karamin sufetan dansanda, Philip Kolo ya gamu da ajalinsa a ranar Laraba 19 ga watan Satumba daidai lokacin da wani jirgin kasa ya bi ta kansa a guje, nan take ya mutu ba ko shuri, inji rahoton jaridar The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kolo ya gamu da ajalin nasa ne akan layin dogo dake gab da babban titin Ikeja a unguwar Oshodi tare da wani dan babur daya dauko a lokacin dayake kan hanyarsa ta zuwa babban ofishin yansandan jahar.

KU KARANTA: Masu zanga zanga sun hana sabuwar ministar kudi shiga Ofis a Abuja

Sufeta Kolo na aiki ne a wata rundunar ta musamman dake karkashin ikon shugaban Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris Kpotun, kuma ya tafi Legas ne don cigaba da wani binciken kwakwaf dayake gudanarwa.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyarmu cewa babu din da dansandan na tsaye ne a gefen layin dogo da nufin idan jirgin y agama wucewa sai dan achaban ya tsallaka layin dogon, sai dai suna tsaye ne sai mayen karfen jirgin ya fizgi babur din, inda tattake dan achaban da dansandan.

Shima wani da lamarin ya faru a gabansa ya bayyana cewa jama’a da dama sun gargadi dan achaban daya koma baya a lokacin da jirgin ya fara matsa na’urarsa mai kara, amma duk dan achaban yayi kunnen uwar shegu dasu.

Kaakakin rundunar yansandan jahar, Chike Oti ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace tuni yansandan jirgin kasa suka fara gudanar da binciken lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel