Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun maka wani dan takarar gwamna a PDP kotu

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun maka wani dan takarar gwamna a PDP kotu

- 'Yan sandan Najeriya sun maka wani dan takarar gwamna a PDP kotu

- Yan sandan sun ce yayi karya da kuma shigar sojan gona

- Sun ce bai yi jarabawar NECO ba

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun shigar da kara a wata kotun tarayyar Najeriya suna kalubalantar dan takarar zama gwamnan jihar Osun a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Sanata ademola Adeleke.

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun maka wani dan takarar gwamna a PDP kotu

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun maka wani dan takarar gwamna a PDP kotu
Source: UGC

KU KARANTA: An garkame Sakatariya jam'iyyar APC ta wata jihar Arewa

Laifukan da jami'an 'yan sandan ke tuhumar Sanatan dai sun hada ne da satar ansa a jarabawa, zamba cikin aminci, zama sojan gona da kuma tafka assha a lokacin yana makarantar Sakandare din sa.

Legit.ng haka zalika ta samu cewa shugaban makarantar gaba da Sakandare ta Ojo-Aro dake a karamar hukumar Egbedore a jihar ta Osun tare da wasu da ake zargin suna da hannu a wajen taimakawa wanda ake tuhumar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan na Najeriya Mista Jomoh Moshood ya shaidawa 'yan jarida cewa Sanata Adeleke din tare da kanin sa Sikiru Adeleke sun zaura jarabawar NECO ne a shekarar 2017 inda sukayi shigar burtu.

A wani labarin kuma, Wani binciken da aka gudanar yana nuni ne da cewa akalla mutane 123 ne suka sayi fom din neman tikitin takarar gwamna a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya a zaben gama gari da za'a gudanar a shekarar 2019.

Mun samu wadannan alkaluman ne daga wata majiyar mu a babbar hedikwatar jam'iyyar ta PDP dake a garin Abuja bayan da aka sanar da rufe saida fom din a satin da ya gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel