2019: Wata kungiya a Arewa ta kada gangar goyon bayan shugaba Buhari

2019: Wata kungiya a Arewa ta kada gangar goyon bayan shugaba Buhari

Kungiyar bayar da tallafi mai suna Modibbo Haruna Buhari Charity Organisation (BCO) ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda tace ya cancanci sake shugabanci karo na biyu.

Mista Madibbo Suleiman-Masaka, shugaban kungiyar na kasa, ya bayyana hakan a hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Keffi, karamar hukumar Keffi dake jihar Nasarawa a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba.

Suleiman-Masaka ya bayyana cewa ayyukan Buhari ya taba rayuwan ‘yan Najeriya kai tsaye.

2019: Wata kungiya a Arewa ta kada gangar goyon bayan shugaba Buhari

2019: Wata kungiya a Arewa ta kada gangar goyon bayan shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Ya kuma kada gangar goyon baya ga tazarcen Buhari, inda yayi bayanin cewa goyon bayansu ya samo asali ne dalilin nasarorin da ya samu ta fannin tsaro, yaki da rashawa, nomad a tattalin arziki da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Kwastam sunyi babban kamu a Gombe inda suka wace tramadol da Diazepam na N7m

A baya Legit.ng ta tattaro cewa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zamo jarumi kamar Ghandi, Mao Zedong da Mandela da irin wannan goyon baya da yake samu daga yan Najeriya da kuma tsarin siyasar jam’iyyar APC.

“Abunda ke faruwa a APC a yanzu zai yi mana kyau. Muna cire bara gurbi sannan muna samun tsarkaku a matsayin jam’iyyar siyasa. Muna gina jam’iyya da tunani mai tsari sannan muna da shugaba mai hangen nesa (Buhari), wadda zai kawo chanji mai aminci,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel