Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dakatar da Sifetan yan sanda daga binciken takardun Sanata Adeleke

Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dakatar da Sifetan yan sanda daga binciken takardun Sanata Adeleke

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sifetan 'yan sanda daga gayyatar Sanata Ademola Adeleke don tuhumarsa

- A safiyar yau ne rundunar yan sanda ta gayyaci Adeleke don amsa wasu tambayoyi

- Buhari ya dakatar da gayyatar har sai bayan kammala zaben jihar Osun

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sifetan 'yan sanda (IGP), Ibrahim Idris, daga gayyatar dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar APC Sanata Ademola Adeleke don tuhumarsa.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa da ta bukaci a sakaya sunanta ya tabbatar da wannan lamari ga manema labarai a ranar Larabar nan.

A safiyar yau ne rundunar yan sanda ta gayyaci Sanata Adeleke da ya bayyana a shalkwatar ta don amsa wasu tambayoyi kan zargin da ake yi masa na yin satar amsa, kutse ga rayuwar wani, da kuma cin amana, da dai sauran laifuka.

KARANTA WANNAN: Matakan tantance dan takara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC

Shugaban kasa Buhari ya dakatar da tuhumar Sanata Adeleke

Shugaban kasa Buhari ya dakatar da tuhumar Sanata Adeleke
Source: Facebook

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Ag. DCP Jimoh Mashood, a cikin wata sanarwa ya aikawa Adeleke kiran Sammaci tare da wasu mutane guda hudu; Mr. Sikiru Adeleke, Aregbesola Mufutau (Shugaban makarantar Ojo-Aro Community, karamar hukumar Edbedore, jihar Osun), Mr. Gbadamosi Olutope (Malamin makarantar wanda ya iza wutar aikata laifukan), da su gurfana gaban kwamitin bincike na rundunar da ke Abuja, don kaisu kotu.

A cewar majiyar, Buhari ya bada umarnin dakatar da wannan gayyatar har sai bayan kammala zaben jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

A ranar Asabar mai zuwa ne sanatan zxai kara da Gboyega Oyetola na jam'iyyar APC, Mashood Adeoti na jam'iyyar ADP; Iyiola Omisore na jam'iyyar SDP; Fatai Akinbade na jam'iyyar ADC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel