Buhari ne Ghandi da Mandela dinmu - Ganduje

Buhari ne Ghandi da Mandela dinmu - Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zamo jarumi kamar Ghandi, Mao Zedong da Mandela da irin wannan goyon baya da yake samu daga yan Najeriya da kuma tsarin siyasar jam’iyyar APC.

Ganduje ya yaba ma irin tsarin muli na shugaban kasar da yadda yake tafiyar da lamuran kasar bisa gaskiya da mana

“Abunda ke faruwa a APC a yanzu zai yi mana kyau. Muna cire bara gurbi sannan muna samun tsarkaku a matsayin jam’iyyar siyasa. Muna gina jam’iyya da tunani mai tsari sannan muna da shugaba mai hangen nesa (Buhari), wadda zai kawo chanji mai aminci,” inji shi.

A cewar wata sanarwa dauke das a hannun darakta janar na labaran gwamnatin jihar Kano, Ameen K. Yassar, Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar magoya bayan Buhari suka shirya a babban dakin taron NAF dake Abuja.

Buhari ne Ghandi da Mandela dinmu - Ganduje

Buhari ne Ghandi da Mandela dinmu - Ganduje
Source: UGC

Yace hangen nesa da tsarin shugabancin Buhari ne yasa ya zamo shugaban kasar da zai iya daura kasar akan turbar cigaba.

KU KARANTA KUMA: Kwastam sunyi babban kamu a Gombe inda suka wace tramadol da Diazepam na N7m

Gwamnan ya bayyana cewa ficewar wasu mutane daga APC zai ba jam’iyyar da shugaban kasar damar da zai kawo chanji da yan Najeriya ke bukata sosai.

A cewar Gwamna Ganduje, Buhari na bukatar Karin lokaci domin ya kammala abunda ya fara musamman a fannin dawo da tattalin arziki, tssaron kasa da kuma yaki da rashawa, yace musamman yaki da rashawa aiki ne dake cin lokaci sosai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel