Wata tsiya sai a kasar nan: An 'sace' jirgi guda a filin jirgin Legas

Wata tsiya sai a kasar nan: An 'sace' jirgi guda a filin jirgin Legas

- Abun mamaki, an sace jiragen sama har biyu

- Hakan zai iya tsorata masu zuba hannayen jari

- Wannan ma wani nau'in rashin tsaro ne

Wata tsiya sai a kasar nan: An 'sace' jirgi guda a filin jirgin Legas

Wata tsiya sai a kasar nan: An 'sace' jirgi guda a filin jirgin Legas
Source: Depositphotos

Jirage biyu masu kirar Bombardier Dash 8 Q 300, wanda kamfanin Topbrass suka taba amfani dasu aka sace a Legas.

Jiragen saman masu lambar rijista 5N-TBB da 5N-TBC sun zamo silar shari'a tsakanin kamfanonin Lessor, Seagold da Topbrass. Wasu masu ra'ayi a shugabancin kasar nan suka siya jiragen, wanda hakan yaci karo da umarnin babbar kotun tarayya dake Legas.

DUBA WANNAN: Ibrahim Mantu zai sulhunta 'yan PDP a Plateau

Majiyar mu ta gano cewa an sace jiragen daga gurin zaman su ne dake filin jirgin Janar Murtala Muhammed. An ajiye su a Aero Contractors Maintenance and Overhaul, amma an goge lambobin su. Bincike ya nuna cewa ana gyaran su domin shirin fitar dasu daga Legas zuwa wani guri na daban.

Hakan ya kawo damuwa ga masu ruwa da tsaki. Sunce rashin iya kula da dukiyar masu zuba hannayen jari suma matsalolin rashin nagarta ne a wannan Gwamnatin. Inda hakan zai iya firgita kasashen da ke da burin zuba hannayen jari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel