Da duminsa: Jam’iyyar APC ta canja ranakun da zata gudanar da zabukan fitar da ‘yan takara

Da duminsa: Jam’iyyar APC ta canja ranakun da zata gudanar da zabukan fitar da ‘yan takara

A yau, Laraba, ne sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC, Emma Ibediro, ya fitar da takardar sanarwar canja ranakun gudanar da zabukan cikin gida na fitar da ‘yan takara a jam’iyyar.

Zaben fitar da dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar ta tsara yi ranar Aljhamis, 20 ga watan Satumba ya koma ranar Talata, 25 ga watan Satumba, yayin da na ‘yan takarar ya koma ranar 29 ga watan Satumba.

Kazalika zaben fitar da ‘yan takarar majalisar dattijai da wakilai ya koma ranar 2 da 3 ga watan Oktoba, yayin da na ‘yan majalisar dokokin jihohi ya koma ranar 4 Oktoba.

Da duminsa: Jam’iyyar APC ta canja ranakun da zata gudanar da zabukan fitar da ‘yan takara

Taron masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC
Source: Facebook

Za a gudanar da taron gangamin tabbatar dad an takarar shugaban kasa na jam’iyyar ranar 6 ga watan Oktoba, kamar yadda yake tun farko cikin tsare-tsaren da APC fitar.

Jam’iyyar ta APC ba ta bayar da wani dalili na daga zabukan ba, sai dai rahotanni sun bayyana cewar hakan ba zai trasa nasaba da batun tantance ‘yan takarar jam’iyyar ba, wanda har yanzu ba a fara ba.

DUBA WANNAN: Duk kanwar ja ce: Tsohon shugaban PDP da ya fita daga APC ya fadi matsalolin jam'iyyun

Kazalika, har yanzu uwar jam’iyyar APC bat a kafa kwamitin da zai gudanar da zabukan fitar da ‘yan takarar ba.

An samu rabuwar kai a jihohi da dama a kan hanyar da jam’iyyar ta APC zata yi amfani da ita wajen fitar da ‘yan takarar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel