Wadanda da za su nemi Gwamnan Jihar Legas tare da Ambode a zabe mai zuwa

Wadanda da za su nemi Gwamnan Jihar Legas tare da Ambode a zabe mai zuwa

Yayin da zaben 2019 ya ke karasowa, mun kawo maku jerin Mutanen da ake tunani za su nemi Gwamnan Jihar Legas inda kujerar Akinwumi Ambode ta ke rawa bayan ya samu matsala da babban Jigon APC Bola Tinubu.

Wadanda da za su nemi Gwamnan Jihar Legas tare da Ambode a zabe mai zuwa

Agbaje, Hamzat za su gwabza da Gwamna Ambode a Legas
Source: Depositphotos

Ga jerin wadanda su ke harin kujerar Ambode nan kamar haka:

1. Femi Hamzat

Dr. Kadri Obademi Hamzat ya yanki fam din takaran Gwamna karkashin APC a 2019. Tsohon Kwamishinan kimiyyan yayi aiki da Bola Tinubu da kuma Tunde Fashola kafin ya nemi Gwamna a 2015 a Jam’iyyar APC inda ya sha kashi wajen Ambode.

2. Jimi Agbaje

Dazu nan mu ka ji cewa ‘Dan takarar Gwamnan Legas Agbaje wanda ya nemi kujerar a baya yace da shi za ayi a 2019. Agbaje yana cikin manyan PDP har ya nemi Shugaban Jam’iyya kwanan nan. A zaben 2015 Agbaje ne ya doke Musliu Obanikoro a PDP.

KU KARANTA: Ambode na fama da muguwar barazana daga Tinubu

3. Jide Sanwo-Olu

Babajide Sanwo-Olu yana cikin wadanda za su kawowa Ambode cikas a APC domin kuwa yana tare da manyan Jam’iyyar da kuma Majalisar Jihar a dalilin mara masa baya da tsohon Gwamna Bola Tinubu yayi. Sanwo-Olu ya rike Kwamishina sau 3 a Legas.

4. Femi Otedola

Wani wanda ake tunani zai iya kawowa shirin tazarcen Ambode matsala shi ne Femi Otedola. Otedola rikakken Attajiri ne wanda Iyayen sa sun taba yin Gwamna na wani ‘dan lokaci. PDP tana kokarin jawo Otedola domin karbe Legas daga hannun APC a 2019.

5. Akinwumi Ambode

A halin yanzu kujerar Gwamna mai-ci Akinwumi Ambode tana rawa bayan babban Mai gidan sa ya juya masa baya. Tinubu ne dai ya tsaida hannun Ambode a 2015 bayan Fashola ya kammala mulki. Sai dai yanzu mafi yawan ‘Yan Jam’iyyar ba su tare da Gwamnan.

Dazu kun ji cewa Mai dakin Ambode ta nemi ta lallashi Asiwaju Bola Tinubu domin ceto kujerar Mijin ta. Sai dai hakan bai yiwu ba domin ta gaza nemawa Mijin na ta alfarma a Jam’iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel