Masu zanga zanga sun hana sabuwar ministar kudi shiga Ofis a Abuja

Masu zanga zanga sun hana sabuwar ministar kudi shiga Ofis a Abuja

Kwanaki biyu da fara aiki a matsayin sabuwar ministar kudi, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta fuskanci kalubale na farko a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba inda wasu yan fansho suka gudanar da zanga zanga har ta kai ga sun hana ta shiga Ofis.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan fanshon da suka fito daga ma’aikatar sufurin jirage sun gudanar da zanga zangar lumana ce a ma’aikatar kudi ta Najeriya, akan rashin biyansu hakkokinsu na fansho na tsawon shekaru goma sha hudu.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da manyan Malamai guda 3 a jahar Kaduna

Wannan zanga zangar ta sanya ministar sauka daga motarta inda ta nufi inda masu zanga zangar suka yi dafifi don ta gana dasu tare da sauraron bukatunsu, kuma an yi dace masu zanga zangar sun bata damar yin magana tare da sauraronta da kunnen basira.

Masu zanga zanga sun hana sabuwar ministar kudi shiga Ofis a Abuja

Masu zanga zanga
Source: Depositphotos

A jawabinta, Zainab Shamsuna ta bukaci yan fanshon da su bata lokaci ta samu kwakkwaran bayanai game da hakkokin nasu, sa’annan ta nemi ganawa da shuwagabannin yan fanshon don tsara yadda za’a biya kudade, tunda a cewarta shekaru goma sha hudu ba karamin zango bane, don haka sai dai a biyasu kudaden da kadan da kadan.

Jin hakan yasa shuwagabannin yan fanshon suka mika Ministar takardar dake dauke da hakkokinsu da suka kai naira biliyan 45.3, wanda suka ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a biya tun a shekarar 2017.

Daga karshe yan fanshon sun nemi ministar data bar kofarta a bude don su dinga samun damar tuntubarta akan hakkokin nasu zuwa lokaci lokaci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel