Dan takarar PDP da Ambode ya kayar a 2015 yana son su sake kece raini a 2019

Dan takarar PDP da Ambode ya kayar a 2015 yana son su sake kece raini a 2019

Tsohon dan takarar gwamnan PDP a 2015, Mr Jimi Agbaje ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takarar gwamna a jihar Legas a babban zaben 2019 mai zuwa.

Agbaje ya tabbatar da takarar na sa ne a wata hirar wayan tarho da ya yi da kamfanin dillancin labarai NAN a jihar Legas.

Dan takarar PDP da Ambode ya kayar a 2015 yana son su sake kece raini a 2015

Dan takarar PDP da Ambode ya kayar a 2015 yana son su sake kece raini a 2015

"Da farko bana da ra'ayin sake tsayawa takarar amma na canja ra'ayina saboda mutane da yawa sun bukaci in fito takarar.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

"Na siya fom, na cika kuma na mayar kwanaki kadan kafin a rufe sayar da fom din. Zan fafata a zaben fitar da gwani da sauran masu neman tikitin takarar gwamna a PDP da za ayi ranar Juma'a 28 ga watan Satumba," inji shi.

Agbaje ya ce yana kyautata tsamanin shi ne zai lashe zaben gwamna a jihar Legas idan ya yi nasarar samun tiktin takara a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Ya kuma ce ya yi imanin cewa jam'iyyar PDP za tayi adalci wajen gudanar da zaben fitar da gwanin domin hakan jam'iyyar ta saba yi a baya.

Agbaje yana daya daga cikin wadanda su kayi takarar kujerar Ciyaman na jam'iyyar PDP a 2017 amma Uche Secondus ne ya yi nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel