An samu bulluwar samarin yan damfara da ke yawo da sunan jami'an shirin TraderMoni

An samu bulluwar samarin yan damfara da ke yawo da sunan jami'an shirin TraderMoni

- An samu bulluwar wasu matasan yan damfara a Kano, da ke yawo da sunan jami'an da ke rejistar shirin gwamnatin tarayya na TraderMoni

- Jama'ar jihar na kokonto akan gaskiya ko akasinta na shirin, ganin cewa babu wanda ya samu tallafin kudin tun bayan bullo da shi a jihar

- Rahotanni sun bayyana cewa yan damfarar na karbar N200 zuwa N1500 a matsayin kudin rejistar shiga shirin daga jama'a

An samu bulluwar wasu matasan yan damfara a kwaryar jihar Kano, inda suke yawo da sunan jami'an da ke rejistar shirin gwamnatin tarayya na TraderMoni. Yan damfarar na karbar kudaden jama'a da sunan kudin yin rejistar shiga shirin.

Shirin dai gwamnatin tarayyabce ta bullo da dhi don tallafawa yan Nigeria musamman masu yin kananan kasuwanci don bunkasa tattalin kasuwancinsu ba tare da duba wani banbanci na babba ko karamin dan kasuwa ba ko banbancin akidar siyasa.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka san hanyoyin rejistar shiga shirin na amfani da wannan damar wajen damafarar mutane musamman ma talakawa, ta hanyar karbar kudade daga hannun su da zummar cewa za su taimaka masu wajen rejistar shiga shirin.

Wasu daga cikin jama'ar da suka zanta da wakilinmu sun bayyana damuwar su akan gaskiya ko akasinta na shirin, domin tun da aka bullo da shirin a jihar, babu wanda suka ji duriyar ya samu tallafin kudi daga shirin.

An samu bulluwar samarin yan damfara da ke yawo da sunan jami'an shirin TraderMoni

An samu bulluwar samarin yan damfara da ke yawo da sunan jami'an shirin TraderMoni

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Ta tabbata Adeleke ya zana jarabawar WAEC a 1981

Sun yi zargin cewa kasancewar ba wata hukuma bace taka mai-mai da ke kula da shirin a jihar, hakanne ya tilasta jama'a dafifi a duk wasu wuraren da suka ji cewa ana rejistar shirin, wanda kuma hakan ya baiwa wasu yan damfara damar karbar kudade daga hannun jama'a musamman ma talakawa daga cikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa yan damfarar na karbar N200 zuwa N1500 a matsayin kudin rejistar shiga shirin, tun kafin ma su fara cike bayanan mutum.

Ibrahim Sadiq, daya daga cikin wadanda suka fada komar yan damfarar, wamda ya zanta da wakilinmu ya ce ya yi rejista har sau uku a wurare daban daban, yana mai cewa akwai wanda ya yi rejista a wani waje, wanda ya biya N200 don siyen fom din rejistar shirin, ya yin da wani jami'i ya karbar masa N500.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel