Adadin kudade da Gwamnatin tarayya ta bai wa kowane Jami'in tsaro yayin Zaben jihar Osun

Adadin kudade da Gwamnatin tarayya ta bai wa kowane Jami'in tsaro yayin Zaben jihar Osun

Mun samu rahoton cewa ba tare da bata lokaci ba tuni gwamnatin tarayya ta biya kowane karamin ma'aikacin dan sanda N50,000 dangane da hidima ta musamman da kai kawo da za su aiwatar yayin gudanar da zaben gwamnan jihar Osun.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, a halin yanzu akwai jami'an tsaro na 'yan sanda 18, 426 da gwamnatin ta tanada domin hidima tare da tsayuwar daka kan harkokin zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a ranar Asabar 22 ga wannan wata na Satumba.

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, tuni gwamnatin tarayya ta malala wannan kudade cikin asusun ajiya na banki ga jami'an da za su aiwatar da gagarumar hidima ta zabe a karshen wannan mako.

Adadin kudade da Gwamnatin tarayya ta bai wa kowane Jami'in tsaro yayin Zaben jihar Osun

Adadin kudade da Gwamnatin tarayya ta bai wa kowane Jami'in tsaro yayin Zaben jihar Osun
Source: Depositphotos

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, a yayin da gwamnatin tarayya ta biya N50, 000 ga jami'ai daga mafi kankantar mataki zuwa matakin Sajen. Ta kuma biya kowane jami'in dan sanda N120,000 daga matakin Sufeto zuwa ga mataimakin Sufirtanda, inda ta biya N250, 000 ga Kwamshinonin 'yan sanda 8 da ta dora masu hidima ta lura da harkokin zaben.

KARANTA KUMA: 2019: Jam'iyyar APC za ta fara tantance 'yan takarar ta a yau Laraba

A yayin tuntubar wasu kananan jami'an 'yan sanda biyu, sun bayar da tabbacin su na dafe N50, 000 da gwamnatin tarayya ta riga da biyan su ladan hidimar da za su aiwatar yayin zaben.

Kazalika kwamishinan 'yan sanda na jihar Osun, Mista Fimihan Adeoye, ya bayar da tabbacin wannan lamari inda tuni shima ya dafe dukumar ladan hidimar da zai aiwatar yayin zaben a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel