Yanzu yanzu: Ta tabbata Adeleke ya zana jarabawar WAEC a 1981

Yanzu yanzu: Ta tabbata Adeleke ya zana jarabawar WAEC a 1981

- Hukumar zana jarabawar WAEC ta tabbatar da cewa Sanata Ademola Adeleke ya zana jarabawar WAEC a shekara ta 1981

- Hukumar ta bada wannan tabbacin ne biyo bayan wa'adin da wata babbar kotun tarayya ta bata a ranar 11 ga watan Satumba

Zuwa yanzu za a iya cewa nasara na bayan Sanata Ademola Adeleke, bayan da hukumar da ke kula da zana jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Kudu, WAEC ta tabbatar da cewa dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar PDP a zaben jihar da za'ayi ranar asabar, ya zana jarabawar a 1981.

Hukumar ta bada wannan tabbacin ne biyo bayan wa'adin da wata babbar kotun tarayya da ke Bwari, Abuja, ta bata a ranar 11 ga watan Satumba na gabatar da sakamakon jarabawar dan takarar don sani ya zana ko bai zana jarabawar ba.

A wata takardar rantsuwa sa hukumar ta gabatar, dauke da sa hannun Henry Sunday Adewunmi Osindeinde, wani mataimakin daraktan magatakartan sashen zana jarabawar makarantu a hukumar, ya ce Adeleke ya zana jarabawar a watan Mayu/Afrelu a makarantar sakandiren Ede Muslim da ke kan titi Yidi, garin Ede, dauke da lambar jarabawa 19645 da lambar dalibi 149.

Cikakken labarin na zuwa...

Yanzu yanzu: Ta tabbata Adeleke ya zana jarabawar WAEC a 1981

Yanzu yanzu: Ta tabbata Adeleke ya zana jarabawar WAEC a 1981
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Bakar uwa: Wata mata ta sayar da yaronta akan N350,000 don ta yi shagalin kirsimeti da kudin

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa wata babbar kotu da ke Abuja, ta baiwa hukumar jarabawar WAEC umurnin gabatar da takardar rantsuwa na cewar dan takarar sanatan ya zana jarabawar WAEC a babbar makarantar sakandiren Ede Muslim, da ke jihar Osun, a zangon jarabawa a Mayu/Yuni 1981.

Wannan umurni da kotu ta bayar ya biyo bayan wata kara da abokan karawar Sanatan suka shigar, Wahab Adekunle Raheem da Adam Omosalewa Habeeb, inda suka bukaci kotun ta umurci hukumar WAEC da ta bayyana sakamakon jarabawar Sanata Ademola Nuruddeen Adeleke da wasu mutane biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel