APC ta shirya makarkashiya don tsige Saraki da Dogara – CUPP

APC ta shirya makarkashiya don tsige Saraki da Dogara – CUPP

- Jam'iyyar CUPP tayi zargin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kammala shirye-shirye don tsige Saraki da Dogara

- Gamayyar jam'iyyun sun bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 18 ga watan Satumba

Jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP) tayi zargin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kammala shirye-shirye don tsige Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Gamayyar jam’iyyun da suka hade suka kafa jam’iyyar hadin gwiwa a kokarinsu na ganin sun kayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 sun bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 18 ga watan Satumba.

APC ta shirya makarkashiya don tsige Saraki da Dogara – CUPP

APC ta shirya makarkashiya don tsige Saraki da Dogara – CUPP
Source: Twitter

Ikenga Ugochinyere, kakakin jam’iyyar CUPP ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na shirya makarkashiya domin shigar da korafi kotu inda zasu bukaci kotu da ta sake bude majalisun biyu na dokokin kasar da mambobi kasha daya cikin uku, jaridar The Cable ta ruwaito.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake yawon neman zaben Shugaban kasa a karkashin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Oyo.

KU KARANTA KUMA: Tsayar da Buhari da mayakan Niger Delta suka yi ya tabbatar da karbuwarsa a fadin kasar - BCO

Shugaban Majalisa Saraki yace Shugabannin kasashe da-dama ba su son zuwa kasar nan a yanzu ko kuma su tsere daga zuwan su Najeriya ba tare da sun kammala abin da ya kawo su ba saboda rashin fahimta irin ta Shugaba Buhari.

Saraki yace ana samun hakan ne domin ko kadan Buhari ba ya fahimtar zaman da yake yi da shugabannin kasashen saboda ba ya gane inda su ka dosa don haka wasu manyan Shugabannin ke barin Najeriya da zarar sun zauna da Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel