Bolanle Ambode ta gaza nemawa Gwamna afuwa wajen Tinubu

Bolanle Ambode ta gaza nemawa Gwamna afuwa wajen Tinubu

Har yanzu dai bisa dukkan alamu abubuwa ba su dawo daidai ba tsakanin Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode da kuma wanda ya kawo sa kan kujerar watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bayan lallashin sa ya ci tura.

Bolanle Ambode ta gaza nemawa Gwamna afuwa wajen Tinubu

Matar Gwamna Ambode tayi kokarin ta lallashi Tinubu amma ina
Source: Facebook

Mun sami labari daga Jaridar Punch cewa Matar Gwamnan Jihar Legas Bolanle Ambode ta gana da Bola Tinubu domin nemawa Mai gidan na ta sauki a zabe mai zuwa na 2019. Sai dai Matar Gwamnan ba ta iya shawo kan Tinubu ba.

Patience Ambode ta bi Mai gidan na ta zuwa Garin Osogbo wajen gangamin APC na neman Gwamna inda tayi kokarin ganawa da tsohon Gwamnan Legas Tinubu domin ceto kujerar Mijin ta amma Jigon na APC bai ba ta dama ba.

KU KARANTA: Gwamna Ambode ya sheka Abuja domin shawo kan Tinubu

Labari ya zo mana cewa Matar Gwamnan tayi bakin kokarin ta na ta lallashi Tinubu ya dagawa Ambode kafa amma ya buge da wasanni yana yi mata raha kamar yadda ya saba har ta ji kunya ta hakura. Haka dai Uwargidar Gwamnan ta hakura.

Ana tunani cewa Tinubu za su hana Ambode tsayawa takara a Jam’iyyar APC a 2019. Wasu Jam'iyyu kusan 30 a Najeriya sun shiga cikin rikicin na Ambode da Tinubu inda tuni su ka fadawa Ambode ya zo su ba sa tikiti a sama na zaben badi.

Yanzu dai ana kishin-din Bola Tinubu ya juyawa Ambode baya inda yake neman wani tsohon Kwamishina a Gwamnatin Fashola watau Babajide Sanwo-Olu ya nemi kujerar Gwamnan a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel