Za'a fara tilastawa 'yan Najeriya amfani da lambar dan kasa - FG

Za'a fara tilastawa 'yan Najeriya amfani da lambar dan kasa - FG

- NIMC za ta fara tilastawa 'yan Najeriya amfani da lamban dan kasa wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka daga 2019

- Wannan ya biyo bayan dokar NIMC da FEC ta amince da shi wanda ya bawa NIMC ikon daukan wannan matakin

- Rashin lambar dan kasar zai hana mutum iya amfani da banki, samun lasisin tuki, ishoran lafiya da izinin fita kasashen waje

Direkta Janar na Hukumar yin rajistan dan kasa ta National Identity Management Commission (NIMC), Aliyu Abubakar Azizi ya ce gwamnatin tarayya za ta tilastawa kowanne dan Najeriya amfanin da lambar dan kasa NIN daga watan Janairun 2019.

Za'a fara tilastawa 'yan Najeriya amfani da lambar dan kasa - FG

Za'a fara tilastawa 'yan Najeriya amfani da lambar dan kasa - FG
Source: Instagram

A jiya Talata, shugaban NIMC, Aliyu Aziz, ya sanar da cewa kwamitin zartarwa na kasa FEC ta amince da fara amfani da sabuwar tsarin zamani na Digital wajen karbar bayyanan 'yan Najeriya domin addana su a ma'ajiyar ta kasa.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

Aziz ya ce dokar NIMC ta aka zartar ta baiwa hukumar ikon zabar ranar da za'a fara tilastawa 'yan kasa amfani da lambar ta NIN.

Za'a rika amfani da lambar ta NIN ne wajen yin neman izinin tafiya kasashen waje, inshora ta lafiya, wajen hadadan kasuwanci a bankuna da kuma wajen yin lasisin tuki a Najeriya.

Shugbanan hukumar ya ce daga ranar 1 ga watan Disamban 2018 hukumar za ta fara tattara bayyanan 'yan Najeriya da aka karba a waje guda. Hakan na nuna cewa wanda su kayi rajitsa har zuwa 30 ga watan Nuwamban 2018 ne bayanansu zai samu shiga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel