Tsayar da Buhari da mayakan Niger Delta suka yi ya tabbatar da karbuwarsa a fadin kasar - BCO

Tsayar da Buhari da mayakan Niger Delta suka yi ya tabbatar da karbuwarsa a fadin kasar - BCO

Kungiyar yakin neman zabeen Shugaba Buhari (BCO) sun bayyana cewa tsayar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mayakan Niger Delta suka yi alamu ne dake nuni ga cewa ya samu karbuwa a fadin kasar harma inda jam’iyyar adawa tafi karfi.

Kungiyoyin mayakan karkashin Reformed Niger Delta Avengers (RNDA) a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba sun kaddamar da goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Buhari a 2019, cewa shi ne shugaban kasa guda da ya nuna jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban yankin Niger Delta tunda yah au mulki a 2015.

Kungiyar ta BCO yayin da take mayar da martani akan lamarin ta bayyana cewa duk da kokarin da yan adawa ke yi son ganin Buhari bai shahara ba, tsyar dashi da mayakan suka yi ya nuna cewa ya cimma nasarori a yankin da aka yasar a lokacin da dan yankin ke mulki.

Tsayar da Buhari da mayakan Niger Delta suka yi ya tabbatar da karbuwarsa a fadin kasar - BCO

Tsayar da Buhari da mayakan Niger Delta suka yi ya tabbatar da karbuwarsa a fadin kasar - BCO
Source: Twitter

Daraktan bayanai da tsare-tsare na BCO, Mallam Gidado Ibrahim ya bayyana a wani jawabi da ya saki a Abuja cewa duk da fafutukar da harkowan da mutane Ogoni keyi, gwamnatin da ta gabata taki mayar da hankali a kiraye-kirayen mutanen har said a Shugaba Buhari yah au mulki sannan ya dawwo da ayyukan ci gaba a yankin.

KU KARANTA KUMA: Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050 - Rahoto

A baya mun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake yawon neman zaben Shugaban kasa a karkashin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Oyo.

Shugaban Majalisa Saraki yace Shugabannin kasashe da-dama ba su son zuwa kasar nan a yanzu ko kuma su tsere daga zuwan su Najeriya ba tare da sun kammala abin da ya kawo su ba saboda rashin fahimta irin ta Shugaba Buhari.

Saraki yace ana samun hakan ne domin ko kadan Buhari ba ya fahimtar zaman da yake yi da shugabannin kasashen saboda ba ya gane inda su ka dosa don haka wasu manyan Shugabannin ke barin Najeriya da zarar sun zauna da Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel