Zaben Osun: Oshiomhole ya soki Sanata Adeleke na Jam’iyyar PDP

Zaben Osun: Oshiomhole ya soki Sanata Adeleke na Jam’iyyar PDP

Yayin da ake shirin zaben sabon Gwamna a Jihar Osun, mun samu labari cewa Shugaban Jam’iyar APC mai mulki na kasa baki daya watau Adams Oshiomhole ya caccaki ‘Dan takarar PDP inda yace mulki ba rawan disko bane.

Zaben Osun: Oshiomhole ya soki Sanata Adeleke na Jam’iyyar PDP

Adams Oshiomhole yace Adeleke bai san komai ba sai tika rawa
Source: Instagram

Adams Oshiomhole ya soki wanda Jam’iyyar PDP ta tsaida takara watau Sanata Nuruddeen Ademola Adeleke inda yayi kira ga jama’a su guji zaben wanda bai san komai ba illa iyaka yayi ta tika rawa kamar ‘Dan Mazari.

Shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole a wajen babban taron yakin neman zaben Jam’iyyar mai mulki ya fadawa mutanen Jihar Osun cewa idan su ka zabi ‘Dan takarar PDP zai maida gidan Gwamnati wajen rawa da kida.

KU KARANTA: Ni na shigo da Buhari cikin harkar siyasa a Najeriya - Bafarawa

Oshimhole ya nunawa mutane cewa a wannan lokaci ana neman ‘Dan siyasar da yake da gogewa wajen fannin tattalin arziki ne da kuma sanin aiki ba wanda bai iya komai sai rawa ba inda yake nuni ga Ademola Adeleke na PDP.

Kwamared Adams Oshimhole ya kuma soki Sanatan na Osun ta Yamma wanda yake neman Gwamnan Jihar a zaben da za ayi inda yace ‘Dan takarar ya gaza zuwa yayi mukabala da sauran ‘Yan takara domin rawa kurum ya sani.

Kwanaki ne dai PDP ta samu hada-kan Ademola Adeleke da Akin Ogunbiyi inda su ka amince su yi aiki tare a zabe mai zuwa. Sanata Adeleke wanda ya shahara wajen tika rawa iri-iri ne zai yi takara a karkashin Jam'iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel