An damke yan ‘Kalare’ 28 da laifin fyade da fashi

An damke yan ‘Kalare’ 28 da laifin fyade da fashi

Hukumar yan sandan jihar Gombe ta alanta damke yan ta’addan Kalare 28 kan laifin fyade, fashi da kuma damun jama’a.

Yayinda aka bayyana wadannan yan baranda a jiha, Kwamishanan yan sanda jihar Gombe, Shina Tairu Olukolu, yace hukumar yan sandan ta damkesu ne tare da hadin kan sauran jami’an tsaro.

Yace an damke mutane uku daga cikinsu Abubakar Mohammed, 19; Yusuf Munkaila Dayyabu, 19 bisa ga laifin sace yan mata biyu da musu fyade.

An damke yan ‘Kalare’ 28 da laifin fyade da fashi

An damke yan ‘Kalare’ 28 da laifin fyade da fashi
Source: Twitter

Game da cewar yan sanda, an damkesu ne bayan wani Abdul’aziz Jimoh na Bolari a jihar ya kai kararsu a ranan 20 ga watan Agusta, 2018 cewa matasan sun sace diyarsa yar shekara 16 da kawarta yar shekara 17.

KU KARANTA: An kori dalibai 5 daga makaranta don sun sanya Hijabi

Olukolu ya kara da cewa wasu hudu Adamu Abubakar, 20, Suleiman Mohammed, 20, Yahaya Ibrahim, 19 and Abdullahi Idu, 20, duka yan unguwar Kumo a karamar hukumar Akko sun raunata mutane yayinda wani dan siyasa ke raba kudi.

Ya karashe jawabinsa da cewa an kwace makamai daban-daban a hannunsu. Kana za’a gurfanar da sub a tare da bata da lokaci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel