An kori dalibai 5 daga makaranta don sun sanya Hijabi

An kori dalibai 5 daga makaranta don sun sanya Hijabi

Duk da hukuncin da kotu ta yanke na halalta sanya hijabi a makarantun gwamnati, An kori akalla daliban makaranta Musulmai biyar daga makarantan Boko saboda sun sanya Hijabi a makarantar jihar Legas.

Majalisar koli ta harkar Musulunci a Najeriya karkashin jagorancin mai martaba sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad na biyu sun nuna bacin ranta game da wannan abu dake daliban musulmai ke fuskanta a Najeriya.

Shugabar sashen kare hakkin Hijabi, Mutiat Orolu-Balogun, ta saki wannan jawabi ne a yau Lrb, 19 ga watan Satumba, 2018.

KU KARANTA: An rufe Polytechnic saboda ambaliyar ruwa

Jawabin yace: “Sabuwar shugaban makarantan sakandaren Isolo a jihar Legas, Mrs JO Sadare, ta nuna cewa ba zata amince dalibai su sanya hijabi a makarantan ba duk da cewa dalibai sun kwashe shekaru biyu suna amfani da hijabinsu.”

“Shari’ar kotun daukaka kara tsakanin Asiyar Abdulkareem da gwamnatin jihar Legas ya bayyana cewa dalibai na da hakkin sanya hijabi a ciki da wajen makaranta a fadin jihar Legas kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.”

“Mrs Sadare tana barazana ga dalibai inda take cewa su zabi addini ko Karatun Boko. Wannan take hakkin dan Adam ne.”

“Muna daukan matakin shari’a a yanzu domin kare hakkin yaranmu. Muna kira ga mutan jihar Legas da su nuna mana goyon bayan”.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel