Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050 - Rahoto

Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050 - Rahoto

Rahoton gidauniyar Bill and Melinda Gates na shekara, ta bayyana cewa Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050.

A cewar shafin gidauniyar na yanar gizo, rahoton yayi duba ga nasarorin da aka samu a fadin duniya. A wannan shekarar, daga taron har rahoton zai mayar da hankali akan yawan matasa da zasu shafi cigaban duniya anan gaba.

Rahoton ya bayyana cewa yayinda “sama da mutane biliyan suka tsamo kansu daga tsananin talauci a fadin duniya, tsantsan talauci na karuwa a kasashen Afrika.

Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050 - Rahoto

Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050 - Rahoto
Source: Depositphotos

“A 2050, mutane masu fama da tsantsar talauci a duniya wato kaso 86 cikin dari zasu kasance a yankin ne.”

Daga 2050, sama da kaso 40 cikin 100 na mutane masu fama da kangin talauci a duniya zasu kasance a kasashe biyu ne kawai: jumhuriyar damokradiyyar Cango da Najeriya. Ko a cikin kasashen ne abun zai ta’allaka a wasu yankuna ne.

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki yace Buhari bai fahimtar komai idan ya zauna da Turawa

Rahoton ya nuna cewa yawan mutanen Najeriya zai karu zuwa miliyan 429 a shekarar 2050, inda mutane miliyan 152 zasu kasance cikin talauci.

Sauran kasashen da zasu kasance da matalauta sun hada da Madagascar, Somalia, Burundi, Malawi, Zambia, South Sudan, Central African Republic, da kuma Guinea Bissau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel