Shugaba Buhari ya sake tsokaci kan Leah Sharibu, da ke hannun Boko Haram

Shugaba Buhari ya sake tsokaci kan Leah Sharibu, da ke hannun Boko Haram

- Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen ganin an ceto Leah Sharibu da sauran wadanda Boko Haram ta ke garkuwa da su

- Shugaban kasan ya fadi hakan ne a yayin da ya ke mika sakon ta'aziya game da kisar ma'aikaciyar Red Cross, Saifura Khorsa

- Boko Haram din tayi barazanar kashe Leah Sharibu da sauran ma'aikatan Red Cross da ke hannun ta

Shugaba Muhammadu Buhari ya jadada kokarin gwamnatinsa na ganin cewa an sako sauran 'yan matan Chibok da 'yan sakandare ta Dapchi da ke hannun mayakan Boko Haram ciki har da Leah Sharibu.

Miss Sharibu tana daya daga cikin 'yan mata sama da 100 da 'yan Boko Haram suka sace daga makarantarsu da ke Dapchi a farkon wannan shekarar.

Shugaba Buhari ya sake tsokaci kan Leah Sharibu, da ke hannun Boko Haram

Shugaba Buhari ya sake tsokaci kan Leah Sharibu, da ke hannun Boko Haram
Source: UGC

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

Wasu daga cikin 'yan matan da aka sace a Dapchi sun dawo gidajensu amma ba'a sako Leah Sharibu ba saboda ta tubure ta ki karbar addinin musulunci kamar yadda aka ce.

Shugaban Buhari ya yi wannan alkawarin ne a ranar Talata yayin da ya ke mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan ma'aikaciyar lafiya ta Red Cross, Saifura Khorsa wadda mayakan Boko Haram suka kashe ta cikin kwanan nan.

"Zamu cigaba da kokari domin ganin an sako dukkan mutanenmu da ke hannun Boko Haram. Wannan alkawarin ne da ba za mu saba ba. Ina kira ga sauran abokanmu na kaashen waje su cigaba da bamu taimako da hadin kai," inji Buhari.

Boko Haram din sunyi barazanar kashe sauran ma'aikatan lafiya na Red Cross biyu da ke hannun su har ma da Leah Sharibu a wata sako da suka aike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel