Tsarin N10,000 da gwamnatin APC ke rabawa, me ya banbanta su da tsarin dalolin PDP?

Tsarin N10,000 da gwamnatin APC ke rabawa, me ya banbanta su da tsarin dalolin PDP?

- A yanzu dai samari da 'yan mata masu kasuwanci suna ta darawa saboda sun sami kudin jari daga gwamnati

- Sai dab da zabe masu mulki kan aika wa jama'a kudin 'mun gani muna so'

- Banbancin Jonathan na PDP da Buhari na APC

Tsarin N10,000 da gwamnatin APC ke rabawa, me ya banbanta su da tsarin dalolin PDP?

Tsarin N10,000 da gwamnatin APC ke rabawa, me ya banbanta su da tsarin dalolin PDP?

An gan mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo na bi kusfa kusfa ta kasuwanni da sakunan kasar nan yana rabawa mata masu kasuwanci 'bashin N10,000 wai don su qara jari, cikin tsarin TraderMoni wanda ake sa rai zasu biya nan gaba.

Tsarin N10,000 da gwamnatin APC ke rabawa, me ya banbanta su da tsarin dalolin PDP?

Tsarin N10,000 da gwamnatin APC ke rabawa, me ya banbanta su da tsarin dalolin PDP?

A lokacin mulkin PDP dai, an sha raba jari ko bashi ko kyauta, makudan kudade, wadanda aka yi wa lakabi a 'youwin' da 'yes', da ma sure-p. a baya kuma a lokacin Obasanjo, an ga irin su KEKE NAPEP, da NEEDS da Fadama 1, 2, 3, sai gashi a mulkin APC an sami Trader Moni.

Sai dai mutane na ganin kudaden sunyi kadan, domin jarin N10,000 babu inda zai kai mutum, domin kuwa ko dala 30 bai kai ba.

Matsalar da PDP ta samu, duk da hobbasar da tayi a baya, sai daga karshe ta manta, da zabe yazo, talaka yana gani ana raba daloli amma ga masu sarauta, miliyoyi a jakunkuna, kudade da ake kira kudin makamai.

DUBA WANNAN: Yadda MTN ke fidda biliyoyi daga Najeriya

A wannan karon, duk da kowa ya san matsuwar APC ce ta sanya aka fidda wadannan kudi, domn kar ace har an gama mukin wasu basu ji a kasa ba, domin kuwa a wurin talaka, sai ya amsa sannan yasan anyi aiki.

Idan ma dai kin nan na 'cin hancin zabe' ne za'a iya cewa sun dai fi a baiwa talaka a hannu, maimakon aje a raba wa manyan kasa su amsa su gumtse bakinsu kamar yadda aka yi a 2011 da 2015, shi ko talaka aka yi masa ragin N10 a kudin wuta da na fetur.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel