An rufe Polytechnic saboda ambaliyar ruwa

An rufe Polytechnic saboda ambaliyar ruwa

Hukumar gudanarwa ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha wato Polytechnic da ke Oyo a jihar Anambra sun rufe makarantar, sun kuma umurci dukkan daliban da ke marantar su koma gidajen su a dalilin ambaliyar ruwa da ya mamaye makarantar.

A sanarwar da ya fitar a jiya Talata, mai magana da yawun Kwalejin, Obini Onuchuckwu ya ce an dauki matakin rufe makarantar ne domin kiyaye rayyuka da lafiyar daliban.

"Hanyoyin zuwa makarantar da harabar makarantar da ofisoshi duk sun cika makil da ruwa, dalibai na matukar wahala idan suna son zuwa dakunan karatu.

An rufe Polytechnic saboda ambaliyar ruwa

An rufe Polytechnic saboda ambaliyar ruwa
Source: Twitter

"Ruwa ya mamaye katangar makarantar da na'urar bayar da wutan lantarki wato Transformer wanda hakan ya janyo daukewar wutar lantarki a makarantar," inji shi.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

Mr Onuchuckwu ya yi kira ga hukumar bayar da agajin gagawa na kasa NEMA da hukumar agaji na jihar SEMA su taimakawa kwallejin.

Ya cigaba da cewa, "Muna samun ambaliyar ruwa ko wane shekara amma na bana ya yi tsanani sosai. Baya ga haraban makarantar, har dakunann dalibai da ofisoshin malamai duk sun cika makil da ruwa.

"Ambaliyar ruwa ya lalata kayayakin lantarki da sauran kayan daliban kamar takardu, katifu da sauransu."

Ya ce rashin hanyoyin ruwa a garuruwan da ke makwabtaka da kwalejin ne ya janyo ambaliyar ruwan inda ya tunatar da jama'a cewa irin wannan ambaliyar ruwar da faru a 2012 inda kwalejin ta shafe watanni cike da ruwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel