Rikicin addini da kabilanci sun kare da zarar na samu mulki – Dankwambo

Rikicin addini da kabilanci sun kare da zarar na samu mulki – Dankwambo

Gwamnan Jihar Gombe kuma daya daga cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP watau Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo ya sha kudirin kawo karshen kashe-kashe a kasar nan idan ya samu mulkin Najeriya.

Rikicin addini da kabilanci sun kare da zarar na samu mulki – Dankwambo

Ibrahim Hassan Dankwambo yace zai yi maganin kashe-kashe a Najeriya
Source: Depositphotos

Ibrahim Dankwambo wanda yana cikin manyan ‘Yan takarar PDP a 2019 yayi alkawarin kawo karshen duk wani rikicin addini ko kuma na kabilanci idan harya samu darewa kan kujerar Shugaban kasar Najeriya a 2019.

Gwamnan yayi wa mutanen Numan da aka kashe kwanan nan ta’aiyya ne ta bakin kwamitin yakin neman zaben sa. A karshen makon can ne aka kashe mutane fiye da 50 a Gon, Nzumosu, Bolki, Nyanga da kuma Bukuto.

Ayoade Adewopo wanda shi ne babban Darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Ibrahim Hassan Dankwambo a 2019 yayi tir da wannan abu da ya faru a Garuruwan Adamawa inda yace dole ayi maganin wannan.

KU KARANTA: Za ayi layin dogo daga Kano har zuwa Nijar a Najeriya

Dankwambo yace idan ya samu mulkin kasar nan zai yi irin abin da yayi wajen kawo zaman lafiya a Jihar Gombe. A jawabin na ‘Dan takarar yace zai kawo karshen kashe-kashen da ake yi da sunan addini ko wata kabila kasar.

Gwamna Dankwambo dai yace yayi bakin kokarin sa wajen hana barkewar wani rikici a Jihar Gombe kuma zai yi amfani da irin wannan mataki da ya dauka wajen ganin an samu zaman lafiya a Najeriya idan ya samu mulki.

A baya kun ji cewa wani ‘Dan takarar na PDP Aminu Tambuwal ya sha alwashin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Zamfara, Benuwai, Taraba, da irin su Birnin Gwari idan har aka zabe a a matsayin Shugaban kasa. a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel