Attahiru Bafarawa: Ni na rike hannun Buhari na sanya shi cikin harkokin siyasa

Attahiru Bafarawa: Ni na rike hannun Buhari na sanya shi cikin harkokin siyasa

- Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewar ba abu ne mai sauki ga kowane dan takara ya iya karawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba

- Ya ce shi ne ya kawo Buhari a harkokin siyasa, lokacin da ya bashi tikitin tsayawa takara karkashin ANPP a lokacim da ya ke shugabantar jam'iyyar

- Bafarawa ya ce shi dan arewa ne, kuma Musulmi, wanda shima sunansa Muhammadu, don haka bai ga dalilin da zai hana shi karawa da Buhari ba

Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, ya bayyana cewar ba abu ne mai sauki ga kowane dan takara daga kowace jam'iyya ya iya karawa da shugaban kasa mai ci a yanzu Muhammadu Buhari a babban zabe na 2019 ba.

Bafarawa, wanda ya ke neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP ya bayyana hakan a lokacin da ya gana da Ayo Fayose a Ado-Ekiti.

Tsohon shugaban jam'iyyar ANPP na kasa, ya kalubalanci gwamnati mai ci a yanzu, ya na mai cewa an tafka manyan kura kurai da suka lalata rayukan yan Nigeria, inda ya sha alwashin amfani da kwarewarsa ta siyasa ta shekaru 40 wajen dai-daita kasar idan aka zabe shi a 2019.

Attahiru Bafarawa: Ni na rike hannun Buhari na sanya shi cikin harkokin siyasa

Attahiru Bafarawa: Ni na rike hannun Buhari na sanya shi cikin harkokin siyasa
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: INEC ta ce ba ta haramta amfani da wayar salula a rumfunan zabe ba

"Ba abu ne mai sauki ba dan siyasa ya fuskanci Buhari a zaben 2019, sai dai wadanda suka san Buhari kuma Buhari ya sanni, nima na san shi, kuma na san yadda zan karya lagonsa har na samu nasara akan sa, ma damar aka amince min tare da bani goyon baya.

"Jam'iyyarmu zata samu nasara. Zamu tabbafa an sake gina kasar, an samar da ingantaccen ilimi da kuma bunkasa sauran fannonin.

"Ni dan arewa ne, na fito daga Arewa-maso-Yamma, ni Musulmi ne, kuma sunana Muhammadu, banga dalilin da zai hana yin kara da Buhari ba.

"Ni ne na kawo shugaban kasa Buhari a harkokin siyasa a kasar nan, ni na bashi tikitin da ya tsaya takara a karkashin ANPP a lokacim da na ke shugabantar jam'iyyar ta kasa."

Bafarawa ya ce shi dan siyasa ne, wanda ba zai taba baiwa likitan idanu aikin zuciyarsa ba, yana mai cewa yan Nigeria sun tafka babban kuskure na zabar gwamnatin APC, wanda ya zama wajibi jama'a su canja su don fitar da kasar daga halin ni-yasu da ta ke a ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel