Bukola Saraki yace Buhari bai fahimtar komai idan ya zauna da Turawa

Bukola Saraki yace Buhari bai fahimtar komai idan ya zauna da Turawa

Mun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake yawon neman zaben Shugaban kasa a karkashin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Oyo.

Bukola Saraki yace Buhari bai fahimtar komai idan ya zauna da Turawa

Shugaban Majalisa Saraki yace Buhari ba ya gane ganawar da yake yi da manya
Source: Facebook

Shugaban Majalisa Saraki yace Shugabannin kasashe da-dama ba su son zuwa kasar nan a yanzu ko kuma su tsere daga zuwan su Najeriya ba tare da sun kammala abin da ya kawo su ba saboda rashin fahimta irin ta Shugaba Buhari.

Saraki yace ana samun hakan ne domin ko kadan Buhari ba ya fahimtar zaman da yake yi da shugabannin kasashen saboda ba ya gane inda su ka dosa don haka wasu manyan Shugabannin ke barin Najeriya da zarar sun zauna da Buhari.

KU KARANTA: Jihar Osun ta Jam'iyyar APC ce - Shugaba Buhari

Shugaban Majalisar yace har kuma ta kai Shugabannin Kasar Turai ba su son zuwa kasar nan ko kuma su tsere daga zuwan su Najeriya ba tare da sun kammala abin da ya kawo su ba don haka yace ana bukatar irin sa su yi mulki.

A jawabin na Saraki wanda yake neman Jam’iyyar PDP ta tsaida sa takara a zaben 2019 yace ana bukatar Shugaban kasa ne ‘Dan zamani ba wai mutum irin Buhari ba a wannan mara da Duniya tayi nisa domin ganin Najeriya ta cigaba.

A baya kun ji Bukola Saraki ya kuma bayyana cewa a halin yanzu ba fa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka zaba bane ya ke rike da kasar nan sai dai wasu boyayyu da babu wanda ya san da zaman su ne ke rike da madafan iko.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel