Jama’a sun zabi Buhari amma wani dabam yake mulki – Saraki

Jama’a sun zabi Buhari amma wani dabam yake mulki – Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki wanda yake neman kujerar Shugaban kasa ya bayyana cewa a halin yanzu ba fa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka zaba bane ya ke rike da kasar nan.

Jama’a sun zabi Buhari amma wani dabam yake mulki – Saraki

Saraki yace Shugbaba Buhari bai fahimci mulkin Najeria ba
Source: Depositphotos

Bukola Saraki wanda yake sa ran tika Shugaba Buhari da kasa a 2019 ya bayyana cewa wani boyayyen mutum ne ke rike da madafan iko a kasar nan ba Shugaba Muhammadu Buhari ba. Saraki ya bayyana wannan ne a makon nan a cikin Jihar Oyo.

Shugaban Majalisar yayi wannan jawabi ne a gaban manyan ‘Yan PDP na Kasar Yarbawa lokacin da yake neman su mara masa baya a zabe mai zuwa. Saraki ya kuma ce kabilancin mutanen kasar nan ne ya hana Najeriya nan cigaba gaba daya.

KU KARANTA: Tsohon 'Dan PDP yana cikin masu tantance 'Yan takaran APC

A cewar Saraki, jama’a su na zaben ‘Dan takara ne saboda inda ya fito ba wai abin da zai iya yi wa kasa ba. A dalilin haka yace ake bukatar ‘Yan siyasa irin su a Najeriya masu gogewa kuma wadanda ke da jajircewa kuma su ka san aiki.

Bukola Saraki yace sam Shugaba Buhari bai fahimci shugabanci ba domin kuwa shekaru 3 kenan da ya kafa Gwamnati amma har yanzu babi wani sabon labari. Saraki yace wani dabam ne yake mulkin kasar nan a boye ba Shugaba Buhari ba.

Daya daga cikin ‘Yan takaran PDP na 2019 Bukola Saraki yace ana bukatar Shugaban kasa ne ‘Dan zamani ba wai mutum irin Buhari ba. Saraki yake cewa Shugaban kasar ya raba kan ‘Yan Najeriya bai da cikakkiyar fahimtar mulki ko kadan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel