INEC ta ce ba ta haramta amfani da wayar salula a rumfunan zabe ba

INEC ta ce ba ta haramta amfani da wayar salula a rumfunan zabe ba

- INEC ta ce ba wai ta haramta amfani da wayar hannu a rumfunan zabe bane, sai dai ta haramta amfani da su ne da zaran mutum ya karbi takardar jefa kuri'a

- Ta bayyana hakan ne biyo bayan tofin Allah tsine da PDP ta yi ga hukuncin INEC na haramta amfani da mnayan wayoyi a rumfunan zabe

- INEC ta ce yan Nigeria na sane da irin babban kalubalen da ke tattare da siye da sayar da kuri'u

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ba wai ta haramta amfani da wayar hannu a rumfunan zabe bane, sai dai ta haramtawa masu kada kuri'a amfani da wayoyin ne da zaran sun karfi takardar jefa kuri'a.

Sakataren watsa labarai na shugaban hukumar INEC, Rotimi Oyekanmi, ya warware wannan zare da abawar a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai ma NAN a ranar laraba a Abuja.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan wata samarwa da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uce Secondus ya fitar, na yin tofin Allah tsine ga hukuncin INEC na haramta amfani da mnayan wayoyi a rumfunan zabe.

INEC ta ce ba ta haramta amfani da wayoyin hannu a rumfunan zabe ba

INEC ta ce ba ta haramta amfani da wayoyin hannu a rumfunan zabe ba
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Cikin shekaru 3: Mun tsamo yan Nigeria Miliyan 10 daga talauci - Gwamnatin Buhari

Mr. Oyekanmi ya ce yan Nigeria na sane da irin babban kalubalen da ke tattare da siyen kuri'u da kuma sayar da su, wanda ya yi katutu a zaben da ya gabata.

Ya ce masu ruwa da tsaki sun ta yin kira ga INEC da ta kawo sabbin hanyoyin da za'a dakile siye da sayar da kuri'u a zaben 2019, wannan ne ya sa hukumar ta haramtawa mutane amfani da wayoyi da zaran sun karbi takardar jefa kuri'a, don gudun su dauki hotunan shaidar sayar da kuri'ar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel