Munafuncin siyasa: PDP ta fallasa wani tuggun da su Buhari suka shirya mata a zaben 2019

Munafuncin siyasa: PDP ta fallasa wani tuggun da su Buhari suka shirya mata a zaben 2019

- PDP ta fallasa wani tuggun da su Buhari suka shirya mata a zaben 2019

- Tace akwai dan APC din da ke neman tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar su

- Amma tace ba zai yi nasara ba

Jagoran babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya kuma gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike a ranar Talatar da ta gabata ne dai ya bayyana cewa tuni shi da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar suka gama gano wani tuggun da jam'iyyar APC take shirya masu.

Munafuncin siyasa: PDP ta fallasa wani tuggun da su Buhari suka shirya mata a zaben 2019

Munafuncin siyasa: PDP ta fallasa wani tuggun da su Buhari suka shirya mata a zaben 2019
Source: Facebook

KU KARANTA: An gano inda Nnamdi Kanu ya sulale

A cewar Gwamnan na jihar Ribas, jam'iyya mai mulki ta APC tana nan tana aiki ka'in da na'in ba dare ba rana domin ganin ta sa wani dan jam'iyyar ta su a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar PDP takarar shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa.

Legit.ng ta samu cewa Gwamna Wike ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar Ribas dake a garin Fatakwal lokacin da yake zantawa da manema labarai game da zabukan da jam'iyyar ke shirin fuskanta.

A cewar sa, yanzu dau sun riga da sun gama gano makarkashiyar ta su kuma da yardar Allah ba za suyi nasara a kan su ba domin kuwa za su tabbatar sun kaucewa dukkan sharrin da APC din ke kulla masu.

A wani labarin kuma, Wata kotu a garin Abuja, babban birnin tarayya mun samu cewa ta aikewa da shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma Sanatan dake wakiltar wata mazaba a jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki da sammaci game da fashin bankunan garin Offa.

Kotun dai wadda ke da matsayi na daya tana zaman ta ne a unguwar Lugbe a garin na Abuja kuma ta umurci shugaban jami'an 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris da ya kamomata shugaban majalisar dattawan ya kuma gurfana a gaban ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel