Da dumin sa: Jami'an 'yan sandan Najeriya sun garkame sakatariyar APC a wata jihar Arewa

Da dumin sa: Jami'an 'yan sandan Najeriya sun garkame sakatariyar APC a wata jihar Arewa

- Jami'an 'yan sandan Najeriya sun garkame sakatariyar APC a wata jihar Arewa

- Yan sandan sun ce suna gudun rigima ne

- Jam'iyyar APC a jihar dai ta rabe gida biyu

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Taraba dake a yankin Arewa maso gabashin Najeriya a ranar Talatar da ta gabata ta sanar da daukar matakin rufe sakatariyar jam'iyyar adawa ta All Progressives Congress (APC) a jihar.

Da dumin sa: Jami'an 'yan sandan Najeriya sun garkame sakatariyar APC a wata jihar Arewa

Da dumin sa: Jami'an 'yan sandan Najeriya sun garkame sakatariyar APC a wata jihar Arewa
Source: Twitter

KU KARANTA: Na hannun daman Dogara ya ce bai koma PDP ba

Da yake karin haske game da matakin da suka dauka, kwamishinan 'yan sandan jihar Mista David Akinremi ya bayyanawa manema labarai cewa sun yi hakan ne domin tabbatar da doka da orda tare kuma da kiyaye aukuwar tashe-tashen hankula.

Legit.ng ta samu cewa Kwamishinan, wanda ya zanta da manema labarai a ofishin sa dake a hedikwatar 'yan sandan a garin Jaligo, ya bayyana cea rikicin dake tsakanin masu ikirarin shugabancin jam'iyyar a jihar su biyu ne ya sa suka dauki matakin.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa an fafata kazamin fada a tsakanin magoya bayan El-Suldi da kuma Abdulmumini Vaki dukkanin su masu ikirarin shugabcin jam'iyyar a jihar a ranar Juma'ar da ta gabata.

A wani labarin kuma, Mataimakin kakakin majalisar wakilai a tarayyar Najeriya mai suna Honorabuk Yussuf Lasun a ranar Lahadin da ta gabata ya fito karara ya bayyanawa duniya shi har yanzu yana nan jam'iyyar sa ta All progressives Congress (APC).

Wannan dai kamar yadda muka samu, na zaman tamkar martani ga labaran da suka yi ta yawo a kwanakin baya na cewa mataimakin kakakin majalisar ta tarayya ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel