Albishirin ku ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta yi wani kwarya-kwaryan taro kan karin albashi

Albishirin ku ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta yi wani kwarya-kwaryan taro kan karin albashi

- Gwamnatin tarayya ta yi wani kwarya-kwaryan taro kan karin albashi

- Taron ya samu halartar kusoshin gwamnati

- Satin da ya gabata kungiyar kwadago ta bada sati biyu ga gwamnati

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da marecen ranar Talatar da ta gabata ne dai ya jagorancin wani kwarya-kwaryan taro tare masu ruwa da tsaki na gwamnatin tarayyar Najeriya game da batun karin albashin ma'aikan kasar.

Albishirin ku ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta yi wani kwarya-kwaryan taro kan karin albashi

Albishirin ku ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta yi wani kwarya-kwaryan taro kan karin albashi
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An gano inda Nnadi Kanu ya sulale

Kamar yadda muka samu dai, taron wanda aka gudanar a dakin toron mataimakin shugaban kasar a fadar mulkin ta Villa ya ta'allaka ne kacokam akan yadda gwamnati zata iya tattara kudin da zata biya ma'aikatan sabon tsarin albashin.

Legit.ng ta samu cewa wasu daga cikin mahalarta taron sun hada da sabuwar ministar kudi, Zainab Ahmed, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Udoma Udo Udoma, ministan kasuwanci da saka jari, Okechukwu Enelamah da na kwadago, Dakta Chris Ngige.

Sauran haka zalika sun hada da ministan albarkatun man fetur Ibe Kachikwu da ma sauran shugabannin hukumomin tattara haraji na kasa.

Indai mai karatu bai manta ba zai iya tuna cewa a cikin satin da ya gabata ne hukumar kwadago da kasa ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin sati biyu da su tabbata sun fito da wata kwakkwarar magana game da karin albashin kokuma su gamu da fushin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel