Karo na hudu: Yan majalisar tarayya sun sake gabatar da kudurin gyaran tsarin zabe

Karo na hudu: Yan majalisar tarayya sun sake gabatar da kudurin gyaran tsarin zabe

- Yan majalisar tarayya sun sake gabatar da kudurin gyaran tsarin zabe

- Sau hudu kenan hakan na faruwa

- A baya sau uku Shugaba Buhari na fatali da gyaran

Wani kwamitin hadin gwuiwa tsakanin 'yan majalisar wakilai da na majalisar dattawa game da gyran kundin tsarin zaben Najeriya ya sake gabatar da kudurin gyaran tsarin a karo na hudu bayan shugaban kasa yayi fatali da shi har sau uku a baya.

Karo na hudu: Yan majalisar tarayya sun sake gabatar da kudurin gyaran tsarin zabe

Karo na hudu: Yan majalisar tarayya sun sake gabatar da kudurin gyaran tsarin zabe
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An gano inda Shugaban kungiyar IPOB ya sulale

Kwamitin hadin gwuiwar wanda yayi wani zama na musamman a ranar Talata, ya kuma musanta zargin cewa wai 'yan majalisar sun cire batun na'urar katin zabe a cikin kudurin nasu shi yasa ma shugaba Buhari bai sanya masa hannu ba.

Legit.ng ta samu cewa shugaban kwamitin hadin gwuiwar da kuma ke zaman Sanata a majalisar dattawa Sanata Suleiman Nazif da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman na su yace ya zama tilas gare su su tabbatar an yi gyare-gyaren.

A wani labarin kuma, Mataimakin kakakin majalisar wakilai a tarayyar Najeriya mai suna Honorabuk Yussuf Lasun a ranar Lahadin da ta gabata ya fito karara ya bayyanawa duniya shi har yanzu yana nan jam'iyyar sa ta All progressives Congress (APC).

Wannan dai kamar yadda muka samu, na zaman tamkar martani ga labaran da suka yi ta yawo a kwanakin baya na cewa mataimakin kakakin majalisar ta tarayya ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel