Matsayi: APC ta saka tsohon shugaban PDP cikin masu tantance ‘yan takara a jam’iyyar

Matsayi: APC ta saka tsohon shugaban PDP cikin masu tantance ‘yan takara a jam’iyyar

Jam’iyyar APC a jihar Legas ta kafa kwamitin mutane, da ya kunshi tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Moshood Salvador, da zasu tantance ‘yan takarar neman kujerar majalisar dokokin jihar Legas da za a yi ranar 4 ga watan Oktoba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito shugaban APC a jhar Legas, Alhaji Tunde Balogun, ya rantsar da kwamitin tantance ‘yan takarar yau, Talata, a sakatariyar jam’iyyar dake kan titin ACME.

Ragowar ‘yan kwamitin sun hada da mataimakin gwamnan jihar Legas, Mista Femi Pedro; kwamishinan lafiya, Dakta Jide Idris; jigo a APC a jihar Legas, Mista Wale Oshun; da mamba a kwamitin bayar da shawara, Dakta Abayomi Finnih.

Matsayi: APC ta saka tsohon shugaban PDP cikin masu tantance ‘yan takara a jam’iyyar

Moshood Salvador
Source: UGC

A ranar 27 ga watan Agusta ne tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas, Mista Moshood Salvador, ya bayyana cewar ya koma jam'iyyar APC, kuma a jiya Asabar ne aka yi bikin karbar sa a Legas.

Yanzu haka Salvador tare da wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP sun shiga cikin sahun masu fada a ji a jam'iyyar APC a jihar Legas.

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya lisafa 'yan Najeriya 4 da suka fi Buhari gaskiya da amana

Da yake magana da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) jiya a Legas, Salvador ya ce ya fita daga PDP ne bayan dukkan kokarinsa na dora jam'iyyar a kan hanya ta gari ya ki yiwuwa saboda son rai na wasu dattijan jam'iyyar a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel