Da dumin sa: An gano inda hatsabibi Nnamdi Kanu ya tsere

Da dumin sa: An gano inda hatsabibi Nnamdi Kanu ya tsere

- An gano inda hatsabibi Nnamdi Kanu ya tsere

- An ce ya sulale ya zuwa kasar Ingila ne a birnin Landan

- Tsohon gwamnan jihar Abia ne ya fadi hakan

Tsohon gwamnan jihar Abia dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya Dakta Uzor Kalu a ranar Talata ya bayyana cewa shugaban kungiyar nan ta 'yan kabilar Inyamuran Najeriya dake rajin tabbatar da kafa kasar Biafra watau Independent People of Biafra (IPOB) a turance, Nnamdi Kanu yana birnin Landan.

Da dumin sa: An gano inda hatsabibi Nnamdi Kanu ya tsere

Da dumin sa: An gano inda hatsabibi Nnamdi Kanu ya tsere
Source: Facebook

KU KARANTA: Fashi da makami: Wata kotu ta aikawa Saraki da takardar gayyata

Dakta Kalu dai ya bayyana hakan ne a garin Minna, babban birnin jihar Neja jim kadan bayan ya gama tattaunawar sirri da tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida da ya kaiwa ziyarar ban girma a gidan sa.

Legit.ng da ta samu cewa shi dai shugaban kungiyar ta 'yan Najeriya masu son kafa kasar Biafra a watannin baya ya sulale inda kuma ba'a kara jin duriyar sa ba tun bayan wata hatsaniya da ya jagoranci kungiyar sa da kuma jami'an sojin Najeriya.

A wani labarin kuma, Mataimakin kakakin majalisar wakilai a tarayyar Najeriya mai suna Honorabuk Yussuf Lasun a ranar Lahadin da ta gabata ya fito karara ya bayyanawa duniya shi har yanzu yana nan jam'iyyar sa ta All progressives Congress (APC).

Wannan dai kamar yadda muka samu, na zaman tamkar martani ga labaran da suka yi ta yawo a kwanakin baya na cewa mataimakin kakakin majalisar ta tarayya ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel