Siyasa rigar yanci: Kaakakin majalisa ya tunjuma cikin jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP

Siyasa rigar yanci: Kaakakin majalisa ya tunjuma cikin jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP

A yayin da zabukan shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, yan siyasa daban daban masu muradin tsayawa takarar mukamai daban daban na cigaba da irin nasu lissafin da zai kaisu ga gaci don kada su yi sake a shasu basilla.

Anan ma Kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo, Olagunju Ojo ne ya fice daga jam’iyyar Laour Party zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda jaridar sahara reporters ta ruwaito a ranar Talata 18 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Gwamonin APC 13 sun raka Buhari zuwa jahar Osun a shirin zaben gwamnan jahar

Baya ga Kaakakin majalisar, an samu wasu yan majalisun dokokin jahar guda shidda da suka sauya sheka zuwa jam’iyyu daban daban guda uku, daga ckinsu harda shugaban marasa rinjaye, Ademola Ige.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito akawun majalisar, Paul Bankole ne ya sanar da sauyin shekar yan majalsiun a zaman majalisar na ranar Talata, inda yace Kaakakin majalisa Olagunju ya fice daga jam’iyyar Labour zuwa APC, Wunmi Oladeji, Solomon OluKayode duk sun koma APC daga Labour.

A cigaba da karanto sunayen yan majalisun da suka sauya sheka, akawun majalisar ya bayyana Gbenga Oyekola ya koma jam’iyyar ADC sai kuma Peter Oyetunji ya koma zuwa jam’iyyar PDP, haka zalika dan majalisa Ige da Fatai Adeisina sun fice daga jam’iyyar Accord zuwa jam’iyyar ADC.

Daga karshen zaman majalisar, sia majalisar ta bukaci kwamishinan Yansandan jahar, Abiodun Odude daya kawo karshen fada fadacen yan daba da yan sara suka da suka addabi garin Ibadan na jahar, inda suka ce jama’an garin na zaman dar dar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel