Kalu ya ziyarci IBB, ya nemi ya goya wa tazarcen Buhari baya

Kalu ya ziyarci IBB, ya nemi ya goya wa tazarcen Buhari baya

Tsohon gwamnan jihar Abia, Dr. Orji Uzor Kalu, a ranar Talata, 18 ga watan Satumba ya ziyarci tsohon shugaban kasa a mulki soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a Minna domin nemawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya a kudirinsa na sake takara.

Tsohon gwamnan da tawagarsa sun isa gidan Babangida dake saman tsani da misalin karfe 12:08 na rana cikin bakaken mota kirar Toyota uku da kuma Hillux biyu.

An shigar dashi dakin saukar baki, inda anan ya gana da tsohon shugaban kasar cikin sirri.

Kalu ya ziyarci IBB, ya nemi ya goya wa tazarcen Buhari baya

Kalu ya ziyarci IBB, ya nemi ya goya wa tazarcen Buhari baya
Source: UGC

A wata hira da manema labarai bayan ganawar, wanda ya kwashe tsawon sa’o’i biyu, tsohon gwamnan yace yaje Minna ne domin yin bayani ga tsohon shugaban kasar kan dalilin da yasa ya zama dole a marawa Buhari baya ya yi tazarce.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sultan da shugaban CAN sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2019

A cewar Kalu ya ga ýan takara na PDP na ta tururuwan zuwa ganin IBB don haka sai yaga cewa baza’a barshi a baya ba ya zama dole yaje yayiwa Buhari kamfen.

Da aka tambaye shi kan amsar IBB, tsohon gwamnan yace tsohon shugaban kasar na tunani akai tukuna domin har yanzu da sauran lokaci kafin zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel