APGA ta cika alkawari, ta bawa dan Arewa takarar shugabancin kasa

APGA ta cika alkawari, ta bawa dan Arewa takarar shugabancin kasa

Jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) ta gabatar da Manjo Janar John W.T Gbor mai murabus a matsayin dan takarar shugabancin kasar ta a babban zaben shekarar 2019.

Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar ta kwashe shekaru da dama ba ta tsayar da dan takarar shugabancin kasa kamar yadda bata fitar ba a zaben shekarar 2015.

Ciyaman din jam'iyyar na kasa, Dr Victor Oye ne ya bayar da sanarwan a yau Talata yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a Abuja bayan ya fito daga taron jiga-jigan jam'iyyar a kayi a babban birnin tarayya, Abuja.

APGA ta cika alkawari, ta bawa dan Arewa takarar shugabancin kasa

APGA ta cika alkawari, ta bawa dan Arewa takarar shugabancin kasa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari

Ya kuma bayyana dan kasuwa, dalilin man fetur, Cif Jerry Chukwueke a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar a shekarar ta 2019.

Manjo Janar Gbor dan asalin karamar hukumar Katsina-Ala ne da ke jihar Benue, ya yi aiki a matsayin Kwamandan sashin Ilimi na Sojin Najeriya, shi kuma mataimakinsa Chief Chukuweke dan asalin jihar Imo ne.

"Dan takarar shugabancin kasar mu Manjo Janar din soji ne mai digiri na 3 daga daya daga cikin shahararrun jami'o'in da ke Amurka. Dan takarar mataimakin shugaban kasar mu kuma kwararren ma'aikacin gwamnati ne kuma dan kasuwa da ke digiri a fannin tattalin arziki da kasuwanci," inji Oye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel