Bayan ya aike da wasika, Fayose ya sake aikawa EFCC wani sakon

Bayan ya aike da wasika, Fayose ya sake aikawa EFCC wani sakon

- Gwamna Fayose ya sake amsa wasikar da hukumar EFCC ta aike masa game da gayyatarsa domin amsa tambayoyi

- Fayose ya ce ya nemi hukumar ta dage gayyatar zuwa 16 ga watan Oktoba ne saboda baya son ya sabawa kundin tsarin mulki da ta bashi kariya

- Sai dai gwamna mai barin gadon ya ce idan EFCC ta matsu sai ta same shi a fadar gwamnatinsa a ranar 20 ga watan Satumba

Bayan ya aike da wasika, Fayose ya sake aikawa EFCC wani sakon da fatar baki

Bayan ya aike da wasika, Fayose ya sake aikawa EFCC wani sakon da fatar baki
Source: Twitter

A jiya ne gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya sake rubutawa hukumar EFCC wasika inda ya ce zai samu ikon amsa gayyatar da hukumar tayi masa amma a ranar 16 ga watan Oktoba a maimakon ranar 20 ga watan Satumba da hukumar ta bukaci ya zo.

DUBA WANNAN: 2019: Saraki, Ribadu da Bafarawa sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan salon mulkin Buhari

Fayose ya ce baya son ya saba wa sashi na 308 na kundin tsarin mulkin 1999 ne wadda ta bashi kariya a matsayinsa na gwamna shi yasa ya ke son ya amsa gayyatar kwana daya bayan ya sauka daga mulki.

Gwamna mai barin gadon kuma ya bayyana takaicinsa kan yadda hukumar ta umurci jami'an Kwastam su kama shi idan sun ganshi domin tana tunanin zai gudu bayan wa'addin mulkinsa ya kare, gwamnan ya ce hukumar ne neman lakaba masa laifi tun kafin ayi bincike.

Sai dai daga karshe, Fayose ya ce idan hukumar ba za ta iya jira har lokacin da wa'addin mulkinsa zai kare ba tana iya zuwa ta same shi a ofishinsa da ke jihar Ado-Ekiti a ranar 20 ga watan Satumban 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel