Ya zama dole jihar Osun ta cigaba da kasancewa ta APC - Buhari

Ya zama dole jihar Osun ta cigaba da kasancewa ta APC - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga matanen jihar Osun das u zabi dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar , Alhaji Gboyega Oyetola a zaben ranar Asabar da za’a gudanar.

Ya bayyana hakan a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun a ranar Talata, 18 ga watan Satumba yayinda yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a gangamin da aka shiryawa dan takarar gwamna na jam’iyyar gabannin zaben ranar Asabar.

Buhari ya bayyana dan takarar kujeran gwamna na jam’iyyar a matsayin nagartaccen mutum da ya dace da aikin, yayinda ya bukaci mutanen jihar da su zabi Oyetola domin cigaban ayyukan cigaba da suka gani a gwamnatin Gwamna Rauf Aregbesola.

Ya zama dole jihar Osun ta cigaba da kasancewa ta APC - Buhari

Ya zama dole jihar Osun ta cigaba da kasancewa ta APC - Buhari
Source: Depositphotos

A cewarsa ya zama dole jihar Osun ta cigaba da kasancewa jihar APC domin ganin dorewar ayyukan cigaba da inganci a jihar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, a ranar Talata, 18 ga watan Satumba, ya kaddamar da cewa Jihar Osun bata cancanci dan koyo a matsayin gwamna ba zai wanda zai iya gudu a tseren.

KU KAARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sultan da shugaban CAN sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2019

Oshiomhole ya fadi hakan lokacin da jiga-jigan jam’iyyar karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari suka isa jihar Osun domin yin gangamin karshe don tabbatar da nasarar dan takaransu, Isiaka Oyetola a zaben gwamna da za’a gudanar a jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Oshiomhole yace gwamnati ba wajen da mutun zai koyi aiki bane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel